Majalisar harkokin Shari’ah ta naɗa Sheikh Umar a matsayin sabon shugabanta na kasa

supreme council for sharia in nigeria

Majalisar Koli kan harkokin Shari’ah a Najeriya (SCSN) ta sanar da tabbatar da Sheikh Bashir Umar a matsayin sabon shugabanta na kasa bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyatullah.

A cikin wata sanarwa da Majalisar ta fitar dauke da sa hannun Babban Sakatarenta Malam Nafi’u Ahmed, Majalisar ta bayyana rasuwar Hadiyatullah a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmin Nijeriya da ma wajenta, inda ta yi addu’ar Allah SWT ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Al-Jannatul Firdaus.

Karin karatu: Kotu ta umarci EFCC ta saki Aisha Achimugu cikin sa’o’i 24

Majalisar ta bayyana cewa tabbatar da Umar ya yi daidai da tsarin mulkin da ya kafa Majalisar.

Majalisar ta kara da cewa nan gaba kadan za a sanar da nadin sabon mataimakin shugaba.

Ta kuma bukaci da a ci gaba da addu’a da goyon bayan a daidai lokacin da majalisar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na inganta tsarin addinin Musulunci a fadin Najeriya.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here