Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin ta amince da karin kasafin kudi naira biliyan 215.3 na kasafin kudi na shekarar 2025.
Amincewar ta biyo bayan bukatar da Gwamna Abba Yusuf ya aike tare da karantawa a zauren majalisar a zaman da shugaban majalisar Jibril Falgore ya jagoranta a makon jiya.
Da yake jagorantar zaman, Falgore ya ce majalisar ta yi nazari sosai tare da yin muhawara kan karin kasafin kudin kafin ya zama doka.
Ya ce bangaren majalisar zai tabbatar da sa idon da ya dace a ma’aikatu da hukumomi don tabbatar da yin amfani da kudaden.
An zartas da karin kasafin kudin ne bayan tattaunawa da ‘yan majalisar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Husseini na jam’iyyar NNPP daga Dala, ya ce za a yi amfani da karin kasafin ne domin kula da sabbin ma’aikatu da hukumomin da aka kafa wanda a baya ba sa cikin kasafin kudin farko.
Husseini ya bayyana cewa, za a kuma bayar da wani bangare na kudaden ne domin gyaran makarantu, da inganta ababen more rayuwa da ayyukan sabunta birane.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa kasafin kudin jihar Kano na 2025 a yanzu ya haura sama da Naira biliyan 935.
An ware Naira biliyan 457.08, wanda ya nuna kashi 64 cikin 100 a bangaren kashe kudi, sai kuma Naira biliyan 262.67, wanda ya nuna kashi 36 cikin 100 na kashe kudade na yau da kullum.(NAN)













































