Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci a gaggauta ceto ɗalibai Mata 328 da aka yi garkuwa da su a jihohin Niger da Kebbi

United Nations UN

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan sace ɗalibai da malamai daga makarantar firamare da sakandare ta Katolika ta St. Mary’s da ke jihar Niger, tana mai bukatar a dawo da su cikin gaggawa ba tare da wata barazana ga rayukansu ba.

Wannan lamari ya biyo bayan rahotannin da suka tabbatar da harin da ’yan bindiga suka kai makarantar da ke kauyen Papiri a karamar hukumar Agwara.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta bayyana cewa ɗalibai 303 da malamai 12 ne aka dauke lokacin da maharan suka mamaye makarantar, lamarin da ya kara nuna tsananin barazanar da cibiyoyin ilimi ke fuskanta a yankin Arewa maso Yamma.

Harin ya faru ne makonni kaɗan bayan makamancin lamarin da aka samu a jihar Kebbi.

Karanta: Ƴan sanda sun kama wani da ake zargin yana kera bindigogi ga ’yan ta’adda tare da yi musu safarar su zuwa Kwara

A baya a jihar Kebbi, maharan sun kutsa makarantar sakandaren yan Mata da ke Maga, inda suka dauke ɗalibai akalla 25 kuma suka hallaka malami guda a lokacin harin.

Wannan ya haifar da fargaba kan yadda hare-haren da ake kai wa makarantu ke ƙaruwa ba tare da matakan tsaro tabbatacce ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna goyon baya ga hukumar kare yara ta majalisar da ofishin wakilin jin kai a Najeriya, sannan ta yi kira da a inganta tallafi ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.

Majalisar ta ce dole ne a mayar da hankali kan shirin “Kare Ɗalibai” domin kare makarantu da tabbatar da karatu ba tare da katsewa ba.

A sakamakon wannan hari da sauran tashin hankali a wasu makarantu, gwamnati ta sanar da rufe makarantu 41 na tarayya a fadin ƙasa domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.

Ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa matakin ya zama dole saboda karuwar hare-haren da ake kai wa dalibai.

Majalisar dinkin duniya ta bukaci al’umma su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomi kan duk wani motsi da ba a saba gani ba, tare da tabbatar da cewa duk wani yaro da aka dauke an dawo da shi lafiya cikin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here