Majalisar Dattawa ta gayyaci ministocin kuɗi da ilimi kan rushewar shirin kula da makarantu na Dala Miliyan 30

Senate 1 750x430

Majalisar Dattawa ta hanyar kwamitinta na wucin gadi da ke binciken rushewar shirin ka da inganta Makarantu “safe school initiative” ta umurci ministan kuɗi kuma jagoran harkokin tattalin arzikin ƙasa Wale Edun da ya bayyana a gaban ta mako mai zuwa domin bayani kan yadda shirin ya gaza cimma manufarsa.

Kwamitin wanda Sanata Orji Uzor Kalu na jam’iyyar APC daga jihar Abia ke jagoranta ya yanke shawarar kiran ministan a zaman farko da ya gudanar, tare da tsara kira ga sauran manyan jami’an da ke da rawar gani a shirin ciki har da ministan ilimi Tunji Alausa da ministan tsaro Christopher Musa mai ritaya.

Haka kuma an shirya kiran kwamandan babban hukumar tsaro da kare fararen hula ta ƙasa Dr Mohammed Audi da wakilan masu makarantu domin bayar da bayanai.

Da yake yiwa yan jarida karin bayani yayin rantsar da kwamitin, Kalu ya bayyana cewa majalisar za ta gano duk abin da ya shafi aiwatar da shirin tare da tabbatar da cikakken rikon amana.

Ya kuma bayyana cewa fiye da ɗalibai 1,680 aka sace daga makarantu tun daga 2014, tare da hare-hare a makarantu 180, duk da ware kuɗaɗen da suka haɗa da Dala Miliyan 30 daga 2014 zuwa 2021 da kuma ƙarin naira biliyan 144 da gwamnatin tarayya ta fitar domin ƙarfafa tsaron makarantu.

Kwamitin zai gudanar da bincike kan yadda kuɗaɗen da aka kashe suka kasance da kuma ingancin tsarin aiwatarwa, tare da haɗa ma’aikatu na tarayya, gwamnatocin jihohi, hukumomin tsaro da kungiyoyin farar hula domin gano dalilan da suka hana shirin cimma hakkinsa na kare rayuwar ɗalibai.

Kalu ya jaddada cewa binciken ba ya nufin daidakun mutane ko wata hukuma kai tsaye, sai dai yana da nufin ƙarfafa gaskiya da ingantaccen tafiyar da dukiyar jama’a, domin iyaye a fadin ƙasa suna da hakkin ganin ’ya’yansu na samun ilimi cikin aminci ba tare da tsoron tashin hankali ba.

Binciken ya biyo bayan sabbin rahotannin tayar da hankula a ƙasa sakamakon sace ɗalibai mata 25 a makarantar sakandare da keMaga a jihar Kebbi da kuma fiye da ɗalibai 200 a makarantar St Mary Catholic School a jihar Niger.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here