Majalisar Dattawa ta amince shugaban ƙasa ya ciyo bashin Dala biliyan 2.8 da kuma Dala miliyan 500 na Sukuk

Senate 1 750x430

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar shugaban ƙasa Bola Tinubu na karɓo sabon rancen waje na Dala biliyan 2.847, wanda ya haɗa da Dala miliyan 500 na lamunin Sukuk domin cike gibin kasafin kuɗin shekara ta 2025 da kuma sake biyan tsohon rancen Eurobond na ƙasa.

Amincewar ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan bashi na cikin gida da na waje, ƙarƙashin jagorancin sanata Wamakko Magatarkada Aliyu daga jihar Sokoto, ya gabatar, inda aka yi nazari kan bukatar shugaban ƙasa mai taken “Sabon Rancen Waje da Sake Biyan Lamuni.”

Bisa ga bayani, dala biliyan 2.347 za a samo daga kasuwar kuɗi ta ƙasashen waje domin ɗan rage gibin kasafin kuɗi, yayin da dala miliyan $500 kuma za a samu ta hanyar lamunin Sukuk domin aiwatar da muhimman ayyukan gina ababen more rayuwa a fadin ƙasar.

Amincewar majalisar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa kan hauhawar bashin ƙasar da ya kai sama da naira tiriliyan 97 a tsakiyar shekarar 2025, bisa bayanan ofishin kula da basussuka na ƙasa.

Karin labari: Jami’an hukumar JAMB sun fice daga zaman Majalisar Wakilai saboda halartar ’yan jarida

Duk da damuwar jama’a kan hauhawar bashin, jami’an gwamnati sun ce rancen da aka tsara zai taimaka wajen cike gibin gina muhimman ayyuka da bunƙasa tattalin arziki.

Tun a ranar 8 ga Oktoba ne aka fara karanta wasikar Tinubu a majalisar, inda ya nemi sahalewar majalisar don ɗaukar bashin a matsayin ɓangare na kokarin gwamnati wajen ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan ƙasa da kuma kula da biyan bashin cikin tsarin kasafin shekara ta 2025.

Sanata Wamakko ya bayyana cewa rancen zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki, ci gaba da aiwatar da ayyuka, da kuma kare martabar Najeriya a idon masu bayar da lamuni na duniya.

Sanata Sani Musa daga jihar Neja ya goyi bayan bukatar, yana cewa rancen ya zama wajibi don tabbatar da aiwatar da kasafin kuɗi na shekara ta 2025 yadda ya kamata.

Haka kuma, sanata Adetokunbo Abiru daga jihar Legas ya bayyana cewa wannan sabon rancen ba zai ƙara nauyin bashin ƙasa ba, domin tuni an tanade shi a cikin kasafin kuɗi.

Haka nan, sanata Adams Oshiomhole daga jihar Edo ya ce ɗaukar rance ba laifi ba ne muddin an yi amfani da shi wajen ayyuka masu amfani kamar samar da ayyukan yi da gina ababen more rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here