Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin ɗaurin shekaru 14 ga masu cin zarafin ɗalibai a manyan makarantu

Senate 1 750x430

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin doka da ya tanadar da hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari ga malamai ko ma’aikatan makarantu da aka samu da laifin cin zarafin ɗalibai ta hanyar fasiƙanci a manyan makarantu.

Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar rahotanni kan yadda malamai ke tilasta wa ɗalibai su bayar da kansu don samun sakamako mai kyau ko shiga makaranta ko wasu abubuwan alfarma na karatu.

Kudirin mai suna Dokar Hana Cin Zarafin Dalibai ta Hanyoyin Jima’i (Kariya da Dakilewa), 2025 (HB.1597), an gabatar da shi ne ta hannun mataimakin jagoran majalisa, Sanata Oyelola Ashiru, a zauren majalisar a ranar Laraba domin neman amincewa.

Ashiru ya bayyana cewa kudirin an tsara shi ne domin kare ɗalibai daga duk wani nau’in cin zarafi da ake aikatawa a cikin makarantu, tare da samar da tsayayyen tsarin doka don hukunta masu laifi.

Karanta: Majalisar Dokokin Kano ta fara shirya dokar koyar da ɗalibai da Hausa

Majalisar ta ce duk wanda aka tabbatar da aikata laifin da ke cikin sashe na 4 (1), (2) da (3) na kudirin, zai fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru 14, amma ba ƙarancin shekaru 5 ba, ba tare da zabin tara ba.

Haka kuma, wanda ya aikata laifin da ke cikin sashe na 4 (4), (5) da (6) zai fuskanci ɗaurin shekaru 5, amma ba ƙarancin shekaru 2 ba, ba tare da zabin tara ba.

Kudirin ya kuma bai wa ɗalibai damar kai ƙara idan sun zargi wani da cin zarafi.

A yayin tattaunawa, wasu ɗan majalisa mai wakiltar Edo ta Arewa ya nemi a faɗaɗa kudirin domin ya haɗa da wuraren aiki da sauran fannoni, amma mataimakin shugaban majalisa, Sanata Jibrin Barau, ya bayyana cewa akwai wasu dokoki da ke kula da irin waɗannan lamura a wuraren aiki.

An amince da kudirin, bayan ya zarce karatu na uku domin ya zama doka.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here