Mai shari’a Binta Fatima Nyako ta kotun tarayya reshen Abuja ce za ta saurari karar da Malam Yushau A. Shuaib, wanda shi ne wanda ya kafa kuma mai Mawallafin jaridar PRNigeria, da ya shigar kan cire shi ba bisa ka’ida ba daga cikin mahalarta kwas ɗin manyan jami’ai karo na 47 da cibiyar ƙasa ta dabarun manufofi da nazarin tsare-tsare (NIPSS) ta Kuru ke gudanarwa.
Babban mai shari’a na kotun tarayya, mai shari’a John Tsoho, ne ya bai wa mai shari’a Nyako wannan shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1329/2025, inda za a fara sauraron ta ranar 8 ga Disamba, 2025.
Shuaib na neman kotu ta rushe hukuncin cire shi daga kwas ɗin tare da dawo da shi da duk hakkokinsa, fa’idodi da damar da ke tattare da matsayin nasa.
Shuaib, wanda sananne ne a fannin hulɗar jama’a, ya na neman diyya ta Naira biliyan ɗaya daga cibiyar NIPSS saboda ɓata suna da damuwar da ya fuskanta, da kuma Naira miliyan ɗari a matsayin kuɗin shari’a.
Ya ce an cire shi daga kwas ɗin ne bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da shigar sa, kuma ya biya cikakken kuɗin kwas ɗin Naira miliyan 18.3.
A cikin takardar rantsuwar da ke da sakin layi 40, Shuaib wanda ƙungiyar ƙwararrun masu hulɗa da jama’a (NIPR) ta zaɓa, ya bayyana yadda ya fuskanci tsangwama da cin zarafi ta hanyar bincike da ladabtarwa marar tushe.
Ya kuma ce, an tambaye shi kan labarin PRNigeria mai taken “NIPSS Goes Digital…” wanda ba shi ne ya rubuta ba, da kuma wani ra’ayi da ya gabatar kan “Blue Economy” wanda bai da alaƙa da cibiyar NIPSS.
Ya ƙara da cewa tuhumar da aka yi masa ba ta da tushe a dokar ladabtarwa ta cibiyar, kuma takardar cire shi da aka rubuta ranar 2 ga Yuni, 2025 ba a miƙa masa kai tsaye ba, sai dai aka tura ta ne ga NIPR kawai.
Shuaib ya bukaci kotu ta bayyana cewa NIPSS ba ta da ikon hukunta shi bisa abin da wani kafar labarai mai zaman kanta, PRNigeria, ta wallafa, tunda ba shi ne ya rubuta ko ya amince da labarin ba.
Ya kuma yi zargin cewa matakan da cibiyar ta ɗauka na hana sauran mahalarta hulɗa da shi, da cire shi daga dandamali na hukuma, sun zama nau’in cin zarafi da tsangwama a internet.
Yanzu dai kotu ƙarƙashin mai shari’a Binta Nyako za ta tantance ko matakin da cibiyar NIPSS ta ɗauka kan Shuaib ya yi daidai da doka ko akasin haka.













































