Mahaifin Surajo Rabiu, dan banga daga unguwar Jaba a karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano, wanda aka caka masa wuka a lokacin da yake tare da tawagar Sarki Muhammadu Sanusi II bayan kammala sallar idi, ya bukaci a yi masa adalci tare da neman a biya shi diyya bayan rasuwar dansa.
A wata hira ta musamman da ya yi da SolaceBase a ranar Talata, mahaifin da ke cikin bakin ciki, Muhammadu Rabiu, ya bayyana abubuwan da suka ratsa zuciyarsa sanadiyyar rasuwar dansa.
“A ranar Idi, kafin lamarin ya faru, Surajo yana shirye-shiryen halartar Sallar Idi kamar yadda ya saba, a matsayinsa na ‘yan banga a yankinmu, ana yawan gayyatarsa da ya shiga jami’an tsaro a lokutan bukukuwan jama’a don taimakawa wajen samar da tsaro, sai ya bar gidanmu amma ya dawo kamar minti biyar bayan ya dawo, ya shaida wa mahaifiyarsa cewa ya canza shawara kuma ba zai je ba, sai ya ce mutane sun kawo masa kayan wutar lantarki don gyarawa, amma bayan mintuna 2 da ya fara aiki, sai ya sake sanya rigarsa, ya fita zuwa Sallar Idi ba mu kara jin komai ba sai muka samu labarin rasuwarsa.
Surajo Rabiu yana da shekara 26 kuma shi ne na hudu a cikin ‘ya’yan Muhammad Rabi’u su goma sha biyu.
Labari mai alaƙa: Rikicin ranar Sallah: ‘Yan sanda sun fara bincikar Sarki Sanusi bisa zargin bijirewa dokar hana hawa
“Ɗana ya rasu yana da shekara 26, kuma shi ne ɗa na huɗu a cikin ‘ya’yana goma sha biyu,” in ji Muhammadu Rabiu.
Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Masarautar Kano da su binciki wannan al’amari sosai, a yi adalci, tare da bayar da diyya ga rasuwarsa. Yana aiki ne a matsayin jami’in tsaro, yana kare rayuka da dukiyoyi, kuma ya mutu yana bakin aiki.”
Ya kwatanta dansa a matsayin mai aminci, mai mutuntawa, kuma mai yawan aiki.
“Surajo dan kirki ne, mai biyayya ga bin umarnina, duk wanda ya san shi zai iya tabbatar da halinsa na kirki da mutunta wasu, ya kuma shahara da sana’ar gyaran wutar lantarki.”
Ya kara da cewa dansa ba ya shan taba kuma bai taba alaka da wadanda ba a so. “Maƙwabtanmu za su iya tabbatar da hakan,” in ji shi.
“Muna samun ta’aziyya, amma kuma za mu bi wannan batu tare da shugabannin kungiyar ‘yan banga don fahimtar irin matakan da za su dauka a madadin danmu.”
SolaceBase ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, yayin da masu ibada suka taru a filin Sallar Idi a Kano, an kai wani mummunan hari kan ‘yan banga da ke tare da tawagar Sarki Muhammadu Sanusi II. Harin ya yi sanadin asarar rayuka, wasu da dama kuma sun samu raunuka.
A cewar hukumomin ‘yan sanda, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin