Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta ce ta tabbatar da rashin daidaito a tsarin tafiyar da shirin rancen dalibai.
Daraktan wayar da kan jama’a da ilimi na ICPC, Demola Bakare ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce bayan da aka tabbatar da rashin daidaito a harkokin tafiyar da rancen, hukumar ta kammala shirye-shiryen tsawaita bincikenta zuwa cibiyoyin da za su ci gajiyar tallafin da kuma daidaikun daliban da za su karba.
Bakare ya ce tun da farko hukumar ta yi bincike a kan yadda ake karkatar da kudaden rancen dalibai a karkashin asusun ba da na lamuni na ilimi na Najeriya NELFUND ba.
A cewarsa, binciken ya biyo bayan wani rahoton da kafafen yada labarai suka bayar na cewa akalla manyan makarantu 51 ne ke da hannu wajen cirar kudi da kuma cin gajiyar shirin na NELFUND.
Karin karatu: Ranar Ma’aikata: Tinubu ya sha alwashin ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata
Ya ce ana zargin manyan makarantun da datse kudin da ya kai Naira 3,500 zuwa 30,000 daga kudaden da kowane dalibi ya samu ta asusun lamunin.
Kakakin hukumar ta ICPC ya ce sakamakon farko da aka gudanar ya nuna akwai gagarumin gibi a cikin bayanan kudi na tsarin bayar da kudaden.
Ya ce yayin da aka ce Gwamnatin Tarayya ta saki Naira biliyan 100 na shirin, Naira biliyan 28.8 ne kawai aka raba wa dalibai, inda ya bar Naira biliyan 71.2 da ba a tantance ba.
Bakare ya ce, nan take kwamitin shugaban hukumar na musamman ya dauki matakin da ya dace da karbar rahoton ta hanyar aika wasikun bincike da gayyata ga masu ruwa da tsaki.
Ya ce wadanda aka bayyana sun hada da Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Akanta Janar na Tarayya, da manyan jami’an Babban Bankin Najeriya.
Kakakin hukumar ta ICPC ya ce an kuma gayyaci babban jami’in gudanarwa da daraktoci na NELFUND da su ba da bayanai masu alaka da lamarin. (NAN)