Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta wani raɗe-raɗin yin karba karba da tsohon matamakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Jaridar solaceBase ta rawaito cewa a kwana-kwanan nan, an samu jita-jitar cewa Kwankwaso sun an cimma yarjejeniya tsakaninsa da ragowar yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun hamayyar kasar Atiku na PDP da Peter Obi na LP, kan cewa kowannensu zai yi mulki na wani wa’adi.
Kwankwaso a hirarsa da BBC Imam ya ce bai san da maganar ba, amma ya samu labarin cewa ɓangaren Atikun na ta yin taruka da shugabannin yankin ciki har da malamai, suna faɗa masu wannan magana.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce ”Wannan magana ta ƙona mani rai matuka, a ce dattawa suna ƙarya, suna faɗar abun da ba a yi ba, an faɗa min an tara kusan malamai arba’in da biyar ana gaya masu wannan magana wacce babu ita, ko kaɗan ban ji daɗin wannan abu ba” in ji tsohon dan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP.
Ya kara da cewa ”An gaya musu wai na amince cewa Atiku zai yi shekara hudu, nima zan yi hudu, shi kuma Peter Obi ya yi shekara takwas, wannan maganar babu ita, ba a yi ta ba” in ji Kwankwaso













































