Kwankwaso da Ganduje sun haɗu a karon farko tun bayan zaɓen 2023

WhatsApp Image 2025 11 12 at 21.44.54 750x430

Tsoffin gwamnonin jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun haɗu a karo na farko tun bayan zaɓen 2023.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taron ya gudana ne a gidan tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu, da ke Abuja, inda suka je yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Wannan ganawar ta jawo hankalin jama’a saboda tsawon lokacin da ake fama da sabani tsakanin shugabannin biyu a fagen siyasa.

WhatsApp Image 2025 11 12 at 21.44.54 1 768x626

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta kasance cikin natsuwa da mutunta juna, inda Kwankwaso da Ganduje suka gaisa tare da miƙa ta’aziyyarsu ga tsohon gwamnan Bauchi.

Ana ganin wannan ganawa na iya zama sabon mataki a dangantakar siyasar Kano, musamman ganin yadda rikicin siyasa ya daɗe yana tsamari a tsakanin bangarorin biyu.

WhatsApp Image 2025 11 12 at 21.44.57 768x509

Ganawar ta zo ne kwana guda bayan Ganduje, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa (FAAN), ya gana da gwamnan jihar Kano na yanzu, Abba Kabir Yusuf, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

WhatsApp Image 2025 11 12 at 21.44.55 768x509

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here