Kwamitin Bauchi ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin sarakuna 2 da masarautu 13

Bauchi chiefdoms 750x430

Kwamitin da gwamnatin Bauchi ta kafa kan ƙirƙirar ƙarin masarautu, da sarakuna da yankuna ya ba da shawarar samar da sababbin sarautu guda biyu da kuma ƙirƙirar sabbin majalisun sarauta guda 13.

Shugaban kwamitin, Hamza Akuyam, ne ya bayyana haka a lokacin da suka gabatar da rahotonsu ga gwamna Bala Mohammed a ranar Juma’a a Bauchi.

Ya ce sun yi amfani da tattaunawa da al’umma da masu ruwa da tsaki wajen samar da shawarwarin, inda suka kuma bayar da shawarar ƙara sababbin yankuna 111 a faɗin jihar.

Karanta: Gwamnan Bauchi ya kori Kwamishina a cikin ƙaramin sauyin da zai samar a majalisar zartarwa

A cewarsa, ɗaya daga cikin ayyukan kwamitin shi ne karɓa, nazari da kuma tantance buƙatun al’umma da ke neman ƙirƙirar masarautu, sarautu da yankuna bisa ƙa’idojin da aka sanar wa jama’a, sannan su bayar da shawarwari da za su tabbatar da adalci da haɗin kai.

Akuyam ya ce kwamitin ya karɓi buƙatu 196 daga wuraren da suka haɗa da 17 na neman ƙirƙirar masarautu, 13 na neman ƙirƙirar sarautu da kuma 166 na neman ƙirƙirar sababbin yankuna.

Daga cikin nazari da suka yi, sun ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13 wanda zai ƙara yawan majalisun daga 6 zuwa 19, sannan sababbin sarautu 2 da kuma yankuna 111.

Da yake mayar da martani, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana farin cikinsa kan rahoton, yana mai cewa hanya da dabarun da kwamitin ya yi amfani da su sun gamsar da shi.

Ya ce wannan mataki yana daga cikin alkawuran yaƙin neman zaɓensa domin bunƙasa jihar, samar da ƙarin damar shugabanci da kuma kawar da yankunan da ba a sarrafa su.

Ya ƙara da cewa ƙirƙirar sababbin masarautu, sarautu da yankuna zai taimaka wajen bunƙasa jihar da kuma ƙara kuɗin da ake samu daga asusun tarayya.

Ya ce rahoton za a mika shi ga majalisar dokokin jihar domin yin nazari da aiwatar da shi bisa tsarin doka a cikin lokaci mai ƙanƙanta.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here