Kwamishinan ƴan sanda na Kogi ya kai ziyara ga Gwamna Ododo, tare da alkawarin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tsaron al’umma

WhatsApp Image 2025 11 06 at 20.46.12 750x430

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi, Naziru Bello Kankarofi, ya kai wa Gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ziyarar aiki a ranar Alhamis domin tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ziyarar ta haɗu da ta kwamandan hukumar tsaro ta Civil Depence a jihar, inda jami’an tsaro suka tattauna kan inganta haɗin kai da musayar bayanai a tsakanin hukumomin tsaro.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kogi, CSP William Ovye Aya, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan yadda za a ƙarfafa tsarin tsaron al’umma da samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen hana aikata laifuka a fadin jihar.

A yayin ziyarar, Kwamishina Kankarofi ya yaba wa Gwamna Ododo bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

Ya kuma gabatar wa Gwamnan rahoto kan sabbin matakan tsaro, dabarun hana laifuka, da shirye-shiryen tsaron al’umma da ake shirin aiwatarwa, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro.

Gwamna Ododo ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro, tare da ba su cikakken goyon baya wajen aiwatar da manufofin tsaro da nufin tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar.

Bangarorin biyu sun bayyana kwarin gwiwarsu cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsaro da kyakkyawan yanayi ga al’ummar jihar Kogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here