Ku dakata da cin ganda – Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi yan Najeriya

Ponmo stew 720x430 1
Ponmo stew 720x430 1

Ma’aikatar Noma da Raya Karkara Ta Tarayya, ta sanar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar Anthrax a wasu ƙasashen yammacin Afrika da ke maƙwabtaka da Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Biyo bayan hakan, ma’aikatar ta shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin ganda, naman da aka burara (wanda aka bai wa tsoro da wuta), da namun daji saboda matukar haɗarinsu a yanzu har zuwa a shawo kan lamarin.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Dr Ernest Afolabi Umakhihe, ta ce an fara samun bullar cutar ta Anthrax ne a arewacin Ghana mai iyaka da Burkina Faso da Togo lamarin da ya jefa yankin cikin haɗari.

“Cutar wacce ta yi sanadin rasa rayuka, cuta ce da ke shafar dabbobi da mutane, wato cutar da za a iya ɗauka daga jikin dabbobi.”

“Ana samun ƙwayoyin cutar ta Anthrax ne a cikin ƙasa, kuma galibi ta fi kama dabbobin gida da na daji.”

“Mutane na iya kamuwa da cutar ta Anthrax idan suka yi mu’amala da dabbobin da suka kamu da cutar ko kuma gurbataccen naman dabbobin da ke ɗauke da ita.”

Sai dai kuma ya bayyana cewa, cutar ta Anthrax ba cuta ce mai yaɗuwa tsakanin mutum da mutum ba, saboda haka, ba za a iya kamuwa da ita ta hanyar kusanci da mai cutar ba.

“Alamomin Anthrax kamar na masassara ne, irinsu tari, zazzabi, da ciwon jiki, kuma idan ba a gano cutar da yin maganinta da wuri ba, ta na iya haifar da ciwon huhu matsananci, wahalar numfashi, firgici da kuma mutuwa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here