Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, a matsayin zaɓabɓen gwamnan jihar Gombe.
Kotun mai alkalia uku, dukkansu sun amince cewa jam’iyyar PDP da kuma ADC sun ƙasa tabbatar da zargin da suke yi na aikata ba daidai a zaɓen.
Mai shari’a Orji Abadua, wanda ya jagoranci tawagar alkalan da suka yanke hukuncin, sun amince da hukuncin da kotun sauraron korafin zaɓen gwamnan ta yanke, wadda kuma ta kori ƙarar ɗan takarar jam’iyyar PDP, Jibrin Barde.