Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Gwamnan Filato Muftwang, ta bai wa APC

Caleb Mutfwang Governor of Plateau State
Caleb Mutfwang Governor of Plateau State

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Najeriya ta soke nasarar da Gwamnan Filato Caleb Muftwang ya yi a zaɓen watan Maris na 2023.

Tawagar alƙalai mai mutum uku ta bayyana a ranar Lahadi cewa ba a bi ƙa’ida ba wajen tsayar Mista Muftwang a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP kamar yadda sashe na 285(2) na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Alƙalan sun ce ƙarar da ɗan takarar APC Nentawe Goshwe ya ɗaukaka ta yi nasara saboda batun tsayar da ɗan takara lamari ne da ya shafi lamurran kafin da kuma bayan zaɓe, saɓanin hukuncin da kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta bayar – inda ta bai wa Mista Muftwang nasara.

Tawagar alƙalan ta amince da mai ƙorafin (Goshwe) cewa gazawar PDP na gudanar da bin umarnin wata kotun Filato da ya ce a gudanar da sahihan tarukan jam’iyya a mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma jiha kafin tsayar da ‘yan takara ya saɓa wa doka.

Wannan dalilin ne ya sa kotun ta yi watsi da hukuncin kotun farko a matsayin “wanda bai dace ba kuma ya saɓa da yi wa kowane ɓangare adalci ta hanyar sauraron hujja daga shaidun da aka kora daga shari’ar”.

Kotun ta umarci hukumar zaɓe Inec ta ƙwace shaidar cin zaɓe daga hannun gwamnan mai-ci kuma ta bai wa Nentawe Goshwe na APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here