Kotu Tayi Sammacin Yahaya Bello Akan Zargin Sabuwar Almundahanar ₦110bn.

Yahaya Bello and EFCC 750x430

Jaridar Solacebase ta rawaito Mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun birnin tarayya ta bada sammaci kan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ya halarci kotu don amsa wasu sabbin tuhume-tuhume 16 da ake tuhumar sa.

Kotun tace ta hanyar sammacin ne, tsohon Gwamnan zai halarci kotu a ranar 24 ga Oktoba don amsa wasu muhimman tambayoyi da kuma gurfanar da shi tare da wasu mutane biyu da ake tuhuma.

Mai shari’a Anenih ta bayar da umarnin yin sammacin ne a wani kwarya-kwaryan hukunci da ta yanke biyo bayan bukatar da Hukumar Yaki Da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar.

Mai shari’a Anenih daganan ta umurci hukumar EFCC da ta buga sammacin a wata daga cikin jaridu da ke zagaya a matsayin shaida

Mai Shariar takuma umurci EFCC da ta manna kwafin sammacin da aka yi ga adireshin Bello da kuma a fitattun wurare a harabar kotu.

Hukumar ta EFCC dai ta yi ikirarin cewa ta kasa cimma yadda Bello amsa gayyatar ta bisa tuhumar da aka shigar a ranar 24 ga watan Satumba, inda ake tuhumar tsohon gwamnan da wasu mutane biyu da laifin zamba cikin aminci har naira biliyan N110.4bn.

Sauran mutanen biyu da ake tuhumar su ne Umar Oricha da kuma Abdulsalami Hudu.

Labari ne mai tasowa…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here