Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace guda 753 a Abuja 

753 duplex estate Photo 750x325

Wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ta neman a dawo masa da rukunin gidajen da gwamnati ta ƙwace guda 753 a Abuja 

A ranar 2 ga watan Disamba ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta samu amincewar kotu domin ƙwace unguwa guda mallakar Mista Emefiele da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Unguwar da ke yankin Lokogoma ta ƙunshi gidaje 753.

Tsohon gwamnan ya nemi kotun ta ƙara masa lokaci domin gabatar da buƙatar neman jingine umarnin da ta bayar na ƙwace rukunin gidajen a watan Disamban 2024.

Ya yi iƙirarin cewa bai san lokacin da kotun ta yanke hukuncin ƙwace gidajen ba, sannan ya zargi EFCC da wallafa sanarwar neman mamallakin gidajen a wani “ɓoyayyen sashe na shafin jarida ta yadda zai yi wahala ya iya rubuta martani a kan lokaci”.

Sai dai Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya yi watsi da iƙirarin nasa, yana mai cewa sanarwar da aka wallafa a rabin shafin jarida ta ƙasa ya wadatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here