Kotu ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan Tinubu sakamakon dokar ta-baci da ya sanya a jihar Rivers 

Tinubu Fubara and Amaewhule

Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar da aka shigar kan shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ayyana dokar ta-baci da ya yi a jihar Rivers a ranar 18 ga Maris, 2025.

Wannan matakin na shugaban ƙasa ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida, inda ya naɗa mai kula da jihar guda ɗaya domin jagorantar harkokin gwamnati a lokacin.

Ƙarar dai wacce Belema Briggs da wasu huɗu suka shigar ta yi zargin cewa matakin ya tauye musu ’yancin su.

Sai dai a hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Omotosho ya ce masu shigar da ƙarar ba su da hurumin shigar da ita, saboda irin wannan lamari kotun koli ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci a kai.

Alkalin ya ce masu ƙarar ba su nuna hujja cewa su mambobin majalisar ko gwamnati ne, haka kuma ba su nuna wata illa ta musamman da ta sha bamban da wacce sauran jama’ar jihar suka fuskanta ba.

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa masu ƙarar ba su samu amincewar babban lauyan jihar kafin shigar da ƙarar ba.

Mai shari’a Omotosho ya ƙara da cewa hujjar shugaban ƙasa Tinubu cewa ya ayyana dokar ta-bacin ne don kauce wa rugujewar doka da oda a jihar ba a kalubalance ta ba, balle a tabbatar da akasin hakan.

A ƙarshe, kotun ta bayyana ƙarar a matsayin mara tushe kuma bata lokaci, kasancewar masu shigar da ita ba su da sahihin izini daga jama’ar jihar Rivers don shigar da ƙara a madadinsu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here