Wata kotun majistare da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta gayyaci tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, bisa zarginsa da kin biyan harajin da ya wajaba a kansa na shekarun 2023 da 2024.
Sammacin, mai kwanan watan 21 ga watan Agustan bana, wanda mai shari’a, Chiemena Nonye-okoronkwo, ya umarci Melaye da ya gurfana a gaban kotun da ke Wuse Zone II a ranar 5 ga watan Satumba.
A cewar hukumar tattara Harajin cikin gida ta birnin tarayya Abuja (FCT-IRS), Melaye kuma yana da shari’o’in rashin biyan harajin na shekarun 2020 da 2021 da kuma 2022.
Bayanai da hukumar ta bayar sun nuna cewa tsohon dan majalisar ya biya Naira 85,000.08 a shekarar 2019 sai Naira100,000.08 a shekarar 2020 Sai Naira 120,000 a shekarar 2021, da kuma Naira miliyan 1 a shekarar 2022, duk da cewa ya bayyana karin kudin shiga. Misali a shekarar 2022, an ce Melaye ya bayyana samun kudin shiga na sama da Naira miliyan 6 da dubu ɗari 5 a duk shekara.
FCT-IRS ta ce, an bayar da tantancewar gudanarwa na 2023 da 2024 a ranar 23 ga Mayu, 2025.
Bayan Melaye ya kasa amsa cikin kwanaki 30, an bayar da sanarwar tantance mafi kyawun hukunci a ranar 23 ga watan Yuni.
Sanarwar ta nuna cewa ana bin Melaye bashin Naira miliyan 234.9 na shekarar 2023 da kuma Naira miliyan 274.7 na shekarar 2024.












































