Kotu ta yanke wa masu yunƙurin juyin mulki a Ghana hukuncin kisa

sojin, yanke, kotu, juyin mulki
Wata babbar kotu a Ghana ta yanke wa wasu ‘yan Ghana 6 da suka haɗa da sojoji uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da hannu a wani yunƙurin juyin...

Wata babbar kotu a Ghana ta yanke wa wasu ‘yan Ghana 6 da suka haɗa da sojoji uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da hannu a wani yunƙurin juyin mulki shekaru uku da suka gabata.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi shari’ar cin amanar kasa a Ghana tun shekarar 1966 lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Kwame Nkrumah bayan samun ‘yancin kai.

An kama mutanen 6 ne a shekarar 2021 a lokacin da suke gwajin makamai a babban birnin kasar, Accra, da nufin hamɓarar da gwamnati.

Karanta wannan: Tsohon Gwamnan CBN Sanusi Ya Goyi Bayan Kawo Rukunan Ma’aikata Zuwa Legas

Waɗanda aka yankewa hukuncin, ciki harda mai ƙera bindiga, sun musanta aikata laifin a yayin shari’ar da ta ɗauki hankulan al’ummar kasar.

Lauyoyin da ke kare su sun ce za su daukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.

An saki wasu mutum uku da suka haɗa da babban ɗan sanda daya da wasu sojoji biyu.

An dai jibge jami’an tsaro da yawa a wajen babbar kotun da ke birnin Accra yayin yanke hukunci a ranar Laraba.

Kotun ta samu mutanen shida da laifin cin amanar kasa da haɗa baki wajen aikata babban laifi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here