Kotu ta yanke hukuncin Rataya ga matashin da ya ƙona masallata

Hanging rope 1

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Litinin, ta yanke wa wani mutum mai suna Shafi’u Abubakar, mai shekaru 38 hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma yi masa bulala 150 bisa laifin cinna wa wani masallaci wuta tare da kashe mutane 23.

Abubakar, wanda ke zaune a karamar hukumar Gezawa, a Kano ana tuhumarsa da laifin kisan kai haddasa munanan raunuka da kuma barna ta hanyar tada wuta.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Malam Halhalatu Khuza’i-Zakariyya, ya ce daga cikin shaidu bakwai da masu gabatar da kara suka gabatar, shaidu biyu ne kawai suka tabbatar da lamarin ba tare da wata shakka ba.

Ya ce shaida na 1 da na 2 sai na 3 da na 5 da kuma 6 duk labari kawai suka bayar yayin da ya kawo wani rubutu na addinin Musulunci, da ya ce ba su nan a lokacin da lamarin ya faru ba, labari kawai suka ji, wasu kuma sai suka ga wuta a masallaci.

“Kotu ta amince da shaidar mutum na 4, Ibrahim Salisu, tun da farko ya shaida wa kotun cewa bai ga wanda ake tuhuma ya cinna wa masallacin wuta ba, sai dai ya ga ya na gudu, na amince da hakan a matsayin hujja,” inji shi.

Haka kuma Khuza’i-Zakariyya ya amince da shaidar mutum na 7, Abdullahi Sa’idu, dan sanda, na gabatar da jawabin wanda ake tuhuma. “Konewar da aka gani a hannun wanda ake tuhuma ya kuma nuna cewa ya aikata laifin. a yanzu haka na samu wanda ake kara da laifukan guda hudu,” in ji shi.

Alkalin kotun ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisan kai da kuma yi masa bulala 100 bisa laifin yunkurin kisan kai.

Ya kuma umurci wanda ake kara da ya biya tarar Naira 1,500 saboda ya yi mugun rauni da kuma bulala 50 na tayar da wuta.

Khuza’i-Zakariyya ya kuma umurci gwamnatin jihar da ta karbi babur uku na wanda ake kara a sayar da su domin gyara masallacin da aka kona.

“Wanda ake tuhumar ya na da kwanaki 30 don daukaka kara a hukuncin,” inji shi Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara kuma Darakta a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Salisu Tahir, ya ce wanda ake kara ya aikata laifin ne a kauyen Gadan da ke Larabar Abasawa a karamar Hukumar Gezawa ranar 15 ga Mayu, 2024.

Ya ce a ranar ne wanda ake tuhumar ya je wani masallaci da ke kauyen Gadan Larabar Abasawa, ya zuba fetur ya kuma kunna wuta yayin da mutanen 23 da abin ya shafa ke addu’a da misalin karfe 5:05 zuwa 5:20 na safe. Tahir ya ce da misalin karfe 5:15 na safe, wanda ake kara ya yi yunkurin kashe Shu’aibu Ibrahim da Ibrahim Sani, a lokacin da ya zuba mai tare da cinna musu wuta. “An garzaya da wadanda abin ya shafa asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano sannan mutane 23 sun mutu.”

Tahir ya gabatar da shaidu bakwai na masu gabatar da kara, sannan ya gabatar da bayanan wanda ake tuhuma a cikin harshen Ingilishi da Hausa, da kuma hotunan wadanda aka kashe a baje kolin.Mai shigar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 142, 148, 168 da 370 na dokar shari’a ta jihar Kano, mai lamba 2000.

Sai dai wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Da take mayar da martani, Lauyan tsaro, Hasiya Muhammad-Imam, ta roki a yi masa sassauci a madadin Abubakar, sannan ta bukaci kotun da ta mika shi zuwa babbar cibiyar tsaro ta Janguza.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here