Kotu ta umarci hukumar EFCC ta saki gidaje 27 da ta kwace ba bisa ƙa’ida ba

EFCC operatives

Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta gaggauta sakin gidaje 27 da ta kwace ba bisa ka’ida ba, bayan tabbatar da cewa mallakarsu na da sahihanci.

Alkalin kotun, Justice Joyce Abdulmalik, ce ta yanke wannan hukunci a shari’ar da hukumar ta shigar kan batun kwace dukiyoyi.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hukumar ta samu umarnin wucin-gadi na kwace gidajen a ranar 13 ga Maris, tana zargin cewa an mallake su daga kudaden da bana halal ba.

Kotun ta umarci a wallafa wannan kwace a jarida domin mamallaka su bayyana hujjojin mallaka.

Bayan wallafawa, James Ikechukwu Okwete da kamfaninsa Jamec West Africa Limited suka bayyana a gaban kotu suna tabbatar da mallakar gidaje 26, yayin da Adebukunola Iyabode Oladapo ta tabbatar da mallakar gidan Fandriana Close lamba 12 da ke unguwar Wuse 2 Abuja.

Su duka sun nuna rashin amincewa da kokarin hukumar na neman kwace dukiyoyin dindindin.

Karanta: Tsohon babban Lauya gwamnati Abubakar Malami ya tabbatar da amsa gayyatar hukumar EFCC

A hukuncin da Justice Abdulmalik ta yanke a ranar 31 ga Oktoba, ta amince da bayanan masu gidajen, ta soke bukatar hukumar ta neman kwace gidajen sannan ta rushe umarnin wucin-gadi da aka bayar tun farko.

Ta kuma umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta gaggauta mika takardun mallakar dukkan gidajen ga Okwete da kamfaninsa, tare da mika gidan Fandriana Close lamba 12 ga Adebukunola Oladapo.

Bayan fitar hukuncin, lauyan Okwete da Jamec Ltd, Serekowei Larry, SAN, ya rubuta wa shugaban hukumar takarda yana bayyana cewa hukumar ta ki bin umarnin kotu duk da cewa an kai mata kwafin hukuncin tun ranar 14 ga Nuwamba.

Ya ce ma’aikatan kotu sun ziyarci ofishin hukumar a ranar 26 ga Nuwamba domin aiwatar da hukuncin, amma ta ƙi mika takardun.

Lauyan ya yi gargadin cewa kin bin umarnin kotu na tauye doka ne a tsarin dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa suna sa ran hukumar za ta yi abin da ya dace cikin lokaci kafin daukar matakin doka na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here