Kotu ta umarci a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun Emefiele

Emefiele, Kotu, umarci, ƙwace, dala, miliyan
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bada umarnin a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele...

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bada umarnin a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

Mai shari’a Ayokunle Faji ya yanke hukuncin cewa, an baiwa gwamnatin tarayya kuɗaden ne, biyo bayan buƙatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta shigar.

A baya dai hukumar ta EFCC ta samu umarnin wucin gadi na karɓe kuɗaden a ranar 29 ga watan Mayun 2014.

Karin labari: Daliban sakandire 6 sun nutse a kogi bayan dawowa daga jarrabawa a Kaduna

A zaman kotun, lauyan EFCC, Misis Bilkisu Buhari Bala, ta bayyana cewa kuɗaden sun samu ne ta haramtattun ayyuka da Emefiele ya gudanar.

Umarnin ƙwace kuɗin na dala miliyan 1.4 ya zo ne kwanaki kadan bayan da kotun ta bayar da umarnin a ƙwace kadarorin da suka kai naira biliyan 12.18 daga hannun Emefiele, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here