Kotu ta tsige ɗan majalisa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

APC PDP Logo 750x430

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsige ɗan majalisar wakilai, Abubakar Gummi, bisa sauya sheka daga jam’iyyar (PDP) zuwa (APC).

Gummi na wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta jihar Zamfara a majalisar wakilai.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin, inda ya hana kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ci gaba da karɓar Gummi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazabar.

Kotun ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta shirya sabon zaɓe domin cike gurbin da ya bari a cikin kwanaki 30 daga ranar yanke hukuncin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa an yanke hukuncin a ranar Alhamis, amma an samu cikakken kwafinsa a ranar Juma’a.

Wannan shari’ar dai jam’iyyar PDP ce tare da shugaban jam’iyyar na Zamfara, Jamilu Jibo Magayaki, suka shigar, suna neman kotu ta tabbatar cewa sauya shekar Gummi zuwa APC ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Mai shari’a Egwuatu ya ce babu hujjar da ke nuna cewa akwai rikici a jam’iyyar PDP da zai ba Gummi damar sauya sheka, don haka ya amince da dukkan buƙatun masu shigar da ƙara, ya kuma umarci Gummi da ya mayar wa gwamnatin tarayya dukkan kuɗaɗen albashi da alawus-alawus da ya karɓa daga ranar 30 ga Oktoba, 2024 zuwa ranar yanke hukuncin.

Kotun ta kuma ci tarar Gummi da abokan shari’arsa naira dubu ɗari biyar (₦500,000) tare da bayyana cewa sauya sheka daga jam’iyya zuwa wata don ci gaba da riƙe kujera abu ne da doka ta haramta.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here