Kotu ta sake ɗage sauraren ƙarar da ke neman a hana rabon kananan hukumomi na Kano

High court

Rashin halartar Lauyan tsaro na 9, Cif Adegboyega Awomolo, SAN a ranar Talata ya kawo cikas ga ci gaban shari’ar da ake yi a wata kara da ke neman a dakatar da rabon kudaden da ake baiwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Wadanda suka shigar da karar su ne Abdullahi Abbas, Aminu Aliyu-Tiga, da kuma jam’iyyar APC, ta hannun lauyansu Sunday Olowomoran, suka shigar da kara mai kwanan wata 28 ga Oktoba, sannan suka shigar da kara a ranar 1 ga Nuwamban 2024.

SolaceBase ta ruwaito cewa wadanda ake kara sun hada da Babban Bankin ƙasa (CBN) da kwamitin raba Asusu na rarayya (FAAC), hukumar kula da rarraba Kudi ta (RMAFC) da Akanta-Janar na tarayya, ministan Kudi da babban mai binciken kudi na tarayya, da kuma babban Lauyan tarayya.

Karanta: Kotu ta hana CBN da wasu mutane yin katsalandan a kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Sauran sun hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF) da gwamnatin jihar Kano da babban lauyan Kano da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) da kuma kananan hukumomin Kano 44.

Masu karar na neman a ba da sanarwar cewa wadannan ake kara daga na 12 zuwa 55 ba su gudanar da zabe ta hanyar dimokuradiyya ba duk da doka ce ta kafa su bisa ga sashe na 7 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Suna kuma rokon kotun da ta hana gwamnatin tarayya da babban Bankin ƙasa CBN da kuma babban Akanta nanar su bayar da kudaden da ake rabawa ga kananan hukumomin Kano 44.

A yayin da ake ci gaba da sauraren karar a ranar Talata mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano, ya sanar da kotun cewa lauyan gwamnatin jihar Kano Awomolo ya aike da wasikar neman a dage shari’ar saboda ba ya nan.

“Awomolo ya aiko da wasika yana neman a dage zaman har sai bayan hutun Ista.

Mai Shari’a ya kuma ce, wannan shi ne karo na karshe da zai amince da sake dage shari’arz kasancewar shari’ar ta fuskanci tsaiki sosai kuma shari’ar ba ta aikata laifi ba ce, inda ba da umarnin a gabatar da dukkan matakai kuma a kafin ranar da za a sake zaman.

Amobeda ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 14 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraren karar.

Mai shari’ar yayi karatun baya inda ya tuna cewa irin wannan abu ya faru a ranar 21 ga Janairu saboda lauyan KANSIEC John Baiyeshea bai samu zuwa ba, saboda dalilai na rashin lafiya kuma ya aika da wasika yana neman a dage shari’a.

Tun da farko, lauyan KANSIEC, John Baiyeshea, SAN, ya bukaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar domin samun adalci tunda Awomolo ba ya nan.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Abdul Adamu Fagge, SAN, ya kuma bukaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar domin samun adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here