Kotu ta hana hukumar yaƙi da cin-hanci ta Kano ta binciki naira biliyan 100 da ake zargin an wawushe a kananan hukumomi

Muhuyi Magaji Rimin Gado
Muhuyi Magaji Rimin Gado
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano daga binciken zargin batan Naira biliyan 100 daga asusun kananan hukumomin jihar.
Kotun, karkashin jagorancin mai shari’a S.A. Amobeda, a jiya Talata ta kuma dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da jami’anta daga gayyato, bincike, kamawa, tsoratar da shugabannin kananan hukumomin jihar, har sai an saurari karar da masu nema suka shigar.
Kotun ta ba da umarnin dakatarwa ne a kan buƙatar da Lauyan masu ƙara Morgan C. Omereonye Esq ya gabatar.
A jiya Talata ne dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta fara bincike kan zargin karkatar da kudaden da gwamnatin da ta shude ta Abdullahi Ganduje ta yi.
Hukumar ta yi zargin cewa ta bi diddigin yadda aka karkatar da wasu kudaden har zuwa karshe, cikin shekaru hudu.
Masu shigar da karar su ne shugabannin kananan hukumomin Dawakin Tofa, Ungogo, Dambatta, Kunchi, Rimin Gado, Karaye, Bichi, Tsanyawa, Gwarzo, Tarauni, Dala, Tudun Wada, Kano Municipal da Shanono 15.
Wadanda ake kara kuma sun hada da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, da shugabanta Muhuyi Rimin-Gado.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here