Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC daga karɓar naira miliyan 10 da kuma miliyan 5 daga hannun t ƴan takarar neman shugaban ƙaramar hukuma da kuma Kansila a zaɓen ƙananan hukumomin bana da ke tafe.
Alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwite, ne ya bayar da umarnin a ranar Larabar makon nan.
Solace Base ta ruwaito cewa jam’iyyun Action Peoples Party APP da Action Democratic Party ADP da Social Democratic Party SDP ne suka shigar da ƙarar.
Inda suke ƙarar hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Kano KANSIEC dangane da sanya waɗannan kuɗi a matsayin na shiga zaɓen.
Idan za a iya tunawa dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta dorawa masu neman takarar shugaban ƙaramar hukumar hukuma biyan Naira miliyan 10 yayin da ake sa ran masu neman kansiloli za su biya Naira miliyan 5 a zaben ƙananan hukumomin da aka sake sanya ranar 26 ga watan Oktoban bana.
Tun da farko dai hukumar ta tsara gudanar da zaɓen ne a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Za mu kawo ci gaban labarin a nan gaba.