Kotu ta dage shari’ar kwamandojin ƙungiyar Ansaru guda biyu zuwa 19 ga watan Nuwamba 

Ansaru leaders 750x430

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar kwamandojin ƙungiyar Ansaru guda biyu, Mahmud Usman da Abubakar Abba, zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’ar da ake musu kan zargin ta’addanci.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage zaman bayan rashin halartar lauya mai gabatar da ƙara daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Mohammed Abubakar, wanda ya aike da wasiƙa ga kotu yana neman a dage zaman saboda dalilan rashin samunsa a wancan lokaci.

Lauyoyin da ke kare waɗanda ake tuhuma ba su yi adawa da buƙatar ba, lamarin da ya sa alkalin ya amince da dagewar zuwa ranar da aka tsayar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa a ranar 11 ga Satumba, kotu ta yanke wa Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a ko Abbas Mukhtar, hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari saboda laifin hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, bayan ya amsa laifi ɗaya daga cikin laifuka 32 da ake tuhumarsa da su tare da mataimakinsa Abba, wanda aka fi sani da Isah Adam ko Mahmud Al-Nigeri.

An zargi su da yin hakar duwatsu masu daraja kamar duwatsun thunder da california ba tare da lasisi ba, laifin da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ya sabawa sashi na 8(b) na dokar laifuka dabam-dabam ta shekarar 2004.

Duk da cewa Usman ya amsa laifi a tuhumar da ta shafi hakar ma’adinai, Abba bai amsa laifin ba lokacin da aka karanta masa dukkan tuhume-tuhumen.

Waɗannan kwamandojin biyu na ƙungiyar Ansaru, wacce ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, an gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci da sauran laifuka.

Usman shi ne wanda ake tuhuma na farko, yayin da Abba shi ne na biyu a ƙarƙashin lamba ta FHC/ABJ/CR/464/2025.

A cikin tuhume-tuhumen, an zargi su da taimakawa da shiga cikin ayyukan ta’addanci tsakanin shekarun 2013 da 2015, da kuma zama cikin shugabannin ƙungiyar Jama’atu Ansarul Muslimeena Fii Bilaadis Sudan (Ansaru), wacce aka haramta a Najeriya.

Haka kuma an zarge su da samun horo kan amfani da makamai da kuma kera bama-bamai daga sansanonin ta’addanci daban-daban, da kuma samun horo kan dabarun yaƙi daga ƙungiyar Jama’atu Nusratil Islami Wal Muslimin (JNIM) da ke ƙasar Mali.

An kuma zarge su da hannu a harin da aka kai wa sansanin soja na Wawa da ke Kainji, jihar Neja, a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Bayan sun ƙi amsa laifukan, alkalin ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a ofishin hukumar DSS da ke Abuja har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here