Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 na wucin gadi, waɗanda ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka da ake danganta su da tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, SAN, domin miƙa su ga gwamnatin tarayya.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan lauyan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ekele Iheanacho, SAN, ya gabatar da buƙata ta musamman a gaban kotu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa kadarorin, waɗanda darajarsu ta kai Biliyoyin Naira, suna a birnin Abuja da kuma jihohin Kebbi, Kano da Kaduna.
Ko da yake an bayar da umarnin ne a ranar Talata, an kuma samu kwafin hukuncin da aka tabbatar da sahihancinsa a ranar Laraba.
Mai shari’a Nwite ya yanke hukuncin cewa kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin da aka jero a cikin jadawalin hukuncin, bisa hujjar cewa ana da gamsasshen zargi cewa kadarorin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, don haka za su koma hannun gwamnatin tarayya.
Kotun ta kuma bayar da umarnin wallafa wannan umarni na ƙwace kadarori a wata jarida ta ƙasa, domin gayyatar duk wani mutum ko hukuma da ke da wata fa’ida ko mallaka a kan kadarorin da aka lissafa da su fito su nuna hujja cikin kwanaki 14 daga ranar wallafa sanarwar, dalilin da ya sa bai kamata kotu ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace kadarorin ba.
Karanta: Kotu ta amince da beli ga Malami, matarsa da ɗansa a kan Naira Miliyan 500 kowannensu
Mai shari’a Nwite ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Janairu domin karɓar rahoton bin umarnin kotu.
Daga cikin kadarorin da kotun ta bayar da umarnin ƙwace su na wucin gadi akwai manyan gidaje, otel-otel, filaye, shaguna, da gine-ginen kasuwanci da ke wurare daban-daban, ciki har da Maitama, Asokoro, Wuse, Garki, Jabi, Gwarimpa a Abuja, da kuma Nasarawa GRA a Kano, Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, da Abakpa GRA a Kaduna, tare da wasu kadarori masu daraja ta biliyoyin naira da aka saya a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2024.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya kuma rawaito cewa Abubakar Malami, matarsa Hajia Bashir Asabe, da ɗansa Abubakar Abdulaziz, na fuskantar tuhumar safarar kuɗaɗen haramtattun ayyuka da darajarsu ta kai kimanin naira biliyan 8.7 a gaban kotun Mai shari’a Nwite.
A cikin takardar tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, EFCC ta sanya sunan tsohon ministan, matarsa Hajia Bashir Asabe, ɗansa Abubakar Abdulaziz, da kuma wani ma’aikacin wani kamfani da ake dangantawa da Malami mai suna Rahamaniyya Properties Ltd, a matsayin waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa a cikin tuhuma guda 16, ana zargin waɗanda ake tuhumar da aikata mu’amaloli masu cike da shakku da kuma ƙoƙarin ɓoye asalin kuɗaɗe masu tarin yawa ta hanyar asusun banki da sayen kadarori a Abuja, Kano da Kebbi.
A a zargin laifukan sun faru ne tsakanin shekarun 2015 zuwa 2025, wanda ya haɗa da tsawon shekaru takwas da Malami ya yi yana rike da mukamin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a zamanin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
EFCC ta kuma yi zargin cewa Malami, ɗansa da Hajia Bashir Asabe sun haɗa baki wajen ɓoye asalin kuɗaɗe, mallakar kadarori ta bayan fage, da riƙe kuɗaɗen da suka san cewa sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, wanda hakan ya saɓa wa dokokin hana safarar kuɗaɗen haram na shekarar 2011 da aka yi wa gyara, da kuma dokar shekarar 2022.
A tuhuma ta farko, EFCC ta ce tsakanin watan Yuli na shekarar 2022 da watan Yuni na shekarar 2025, Malami da ɗansa sun umarci kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited da ya ɓoye fiye da Naira Niliyan ɗaya a cikin asusun Sterling Bank, duk da sanin cewa kuɗaɗen sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.













































