Babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan ta amince da jm’iyyar (PDP) ta ci gaba da shirinta na gudanar da babban taron ta na ƙasa a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Alƙali A. L. Akintola ne ya bayar da wannan umarni na wucin gadi wanda ya ba jam’iyyar izinin yin taron a Ibadan kamar yadda aka tsara tun farko.
Kotu ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta halarci taron don sa ido da lura da yadda za a gudanar da shi har zuwa lokacin sauraron ƙarar da ke gaban ta.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wani ɗan jam’iyyar PDP mai suna Folahan Adelabi ya shigar, inda ya nemi kotu ta hana wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar gurbata jadawalin shirye-shiryen taron.
Bayan sauraron ƙarar, alƙali Akintola ya bayyana cewa mai ƙarar ya tabbatar da gaggawar buƙatar shiga tsakani, don haka kotu ta amince da buƙatarsa.
A sakamakon haka, kotun ta hana duk wani yunkurin haifar da cikas ga shirye-shiryen PDP na gudanar da babban taron, tare da umartar manyan jami’an jam’iyyar su tabbatar da an yi taron kamar yadda aka tsara.
Sai dai a baya, babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Alƙali James Omotosho ta dakatar da taron PDP har sai an cika ka’idojin doka da na tsarin jam’iyyar.
Wannan mataki ya haifar da sabani a cikin jam’iyyar, inda wasu manyan jiga-jigai suka bayyana rashin amincewarsu da hukuncin.
Jam’iyyar PDP ta ce hukuncin ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen taron zaben shugabanni ba, tana mai cewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotun tarayya.
A halin yanzu, rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar ya ƙara tsananta yayin da sassan jam’iyyar biyu ke ci gaba da jayayya kan sahihancin shugabanci da ikon gudanar da harkokin jam’iyyar.













































