Wata kotun majistare da ke zamanta a Rijiyar Zaki a nan Kano ta yanke wa Alhaji Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari ko kuma biyan tara sakamakon sare wasu bishiyoyi bakwai a kauyen Sarauniya da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
Solacebase ta rawaito cewa, Lauyar masu gabatar da kara daga tawagar masu sa ido a ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Barista Bahijja H. Aliyu ta samu labarin yadda ake saran itatuwan Neem ba bisa ka’ida ba a kauyen Sarauniya wanda ya sabawa ka’idoji da dokokin muhalli na jihar Kano, wanda hakan ya sa aka gaggauta cafke mai laifin tare da tattara dukkan hujjojin da suka dace kuma aka gabatar da shi a gaban kotu.
A cewar Lauyar, kotun bayan ta duba shaidun da aka gabatar mata ta yankewa wanda ake tuhuma hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu sannan kuma an umarce shi da ya dasa itatuwan Neem 14 a matsayin hukunci na laifin da ya aikata.
Karanta: JAMB: Gwamnatin Kano ta dakatar da duban tsaftar muhalli na watan Afrilu
Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi, Dakta Dahiru M. Hashim, ya yabawa kokarin jami’an sa ido na ma’aikatar da bangaren shari’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen kare muhallin.
Ma’aikatar ta bukaci mazauna yankin da su bi ka’idojin muhalli da ya hana gurɓata muhalli da kuma kai rahoton duk wani abu na lalata muhalli ga hukumomin da suka dace.
Idan za a iya tunawa ma’aikatar muhalli da Sauyin yanayi ta samar da dokokin yaki da gurbata Muhalli da bada kariya ga Dazuka da hana sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, kamar yadda sanarwar da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Isma’ila Garba Gwammaja ya tabbatar.