Kotu ta ɗage sauraron shari’ar zargin almundahanar fiye da Biliyan 1 da ake yi wa shugaban KANSIEC

icpc hq fasad 750x430

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage ƙarar da aka shigar kan Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano, KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da Sakataren Hukumar Malam Anas Muhammed Mustapha, da Malam Ado Garba, Mataimakin Darakta a Sashen harkokin kuɗi na hukumar bisa zargin karkatar da kuɗaɗe sama da Naira Biliyan daya.

SolaceBase ta ruwaito cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta shigar da karar.

A zaman kotun na yau Litinin, lauyan masu gabatar da kara, Barista Enosa Omoghibo, Kuma Mataimakin Daraktan sashen Shari’a na ICPC, ya shaida wa kotun cewa, an shirya gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban kotu amma waɗanda ake tuhumar ba sa gaban kotu.

Sai dai lauyan wanda ake kara, M A. Magaji SAN, wanda ya bayyana tare da A. M. Saleh da Afeez Mahmud da Faheez Mahmud da Kemisola Babatunde da Dino Melaye ga wadanda ake kara, ya ja hankalin kotun cewa babu wani laifi a kan wadanda ake ƙara.

Bayan da kotun ta lura da abin da ya faru, mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 24 ga watan Nuwamban bana, domin gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Idan dai za a iya tunawa, jami’an uku na fuskantar tuhume-tuhume 10 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shigar a kan zargin almundahanar naira biliyan 1 da miliyan 20 a yayin gudanar da zaben kananan hukumomi na shekarar 2024.

A cewar ICPC, mutanen uku sun hada baki ne a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2024 domin yin zamba ta hanyar yin mu’amalar kudade da yawa ba bisa ka’ida ba, ba kuma tare da la’akari da ka’idojin kudi da wasu manyan dokokin da suka haramta almundahana da halatta kudaden haram ba.

A tuhumar da ICPC ta shigar a gaban kotun, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa KANSIEC a ƙarƙashin Farfesa Malumfashi a watan Nuwamban shekarar 2024 kadai, ta karkatar da jimillar kuɗi Naira Biliyan Daya da Naira Miliyan Ashirin kai tsaye daga asusun bankin Unity zuwa na SLM Agro Global Farm, wanda ba shi da wata alaka ta kwangila da KANSIEC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here