Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar da aka gabatar mata don hana hukumar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano gudanar da bincike kan tashar Tsandauri ta Dala Inland Dry Port.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda, ta ƙi amincewa da buƙatar da Hassan Bello, Abubakar Bawuro Sahabo da Adamu Aliyu Sanda suka shigar, inda suka nemi a hana hukumar gudanar da bincike ko kama su saboda zargin da ake yi na binciken mallakar hannun jari a kamfanin Dala Inland Dry Port.
Wadanda suka shigar da ƙarar sun roƙi kotu ta umurci hukumar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano da kuma kwamishinan shari’a na jihar su dakatar da duk wani aiki da ya shafi wannan lamari har sai an kammala sauraron karar da suka shigar kan tauye musu ‘yancin su na asali.
Mai shari’a Amobeda ya ce dole ne a sanar da waɗanda ake ƙara domin su bayyana dalilin da zai sa ba za a amince da wannan buƙata ba yayin sauraron babban ƙarar.
Kotun ta kuma umurci a kai musu takardun shari’ar kafin ranar zaman kotu ta gaba domin su amsa.
An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Oktoba, 2025.













































