Wata babbar kotun majistare a Kano ta yanke wa mutane huɗu hukunci kan laifin sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba a yankin Sharada a karamar hukumar birnin Kano, bisa karya dokokin dajin jihar.
Sanarwar ta fito ne daga ma’aikatar muhalli, inda lauya Barrista Bahijjah H. Aliyu ta gurfanar da Jibril Adamu tare da wasu mutum uku.
Kotun ta same su da laifi.
Mai shari’ar, Auwalu Yusuf, ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, sai dai da zabin biyan tarar naira 40,000 kowanne.
Karanta,: Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Da Shirin Dashen Bishiyoyi Miliyan Uku A Kano
Rahoton ya ƙara da cewa kotun ta kuma umurce su da biyan naira 50,000 a matsayin diyya.
A cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai ta ma’aikatar muhalli, Hajiya Maryam Abdulkadri, ta fitar, ta bayyana cewa laifukan an aikata su ne kafin sabuwar doka ta fara aiki.
Sai dai ma’aikatar muhalli ƙarƙashin kwamishina, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ta bayyana cewa za a yi amfani da tsauraran matakai nan gaba, ciki har da tara har naira 500,000, kwace kayan aiki, da yiwuwar ɗaurin gidan yari ga masu amfani da injin sare bishiya ba tare da lasisi ba.
Hakazalika, masu sare bishiya ba tare da izini ba za su fuskanci tara naira 250,000 kan kowace bishiya, umurnin dasa sabbin bishiyoyi, da kuma yiwuwar kwace kayansu.













































