KNCDC na bincike tare da wayar da kan al’umma a Kano kan zargin ɓullar cutar Mashaƙo da Sanƙarau

IMG 20260201 WA0016 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta hannun Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Jihar KNCDC ta gudanar da ayyukan kula da marasa lafiya, wayar da kan al’umma da kuma tattara samfurori a ƙauyen Gamji da ke Ƙaramar Hukumar Garko, sakamakon rahotannin da suka yadu a kafafen watsa labarai na cewa wasu mazauna yankin sun rasu bisa zargin kamuwa da cutar Mashaƙo da Sanƙarau ta kwakwalwa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an gudanar da wannan aikin ne domin tantance sahihancin rahotannin da kuma duba halin lafiyar al’ummar yankin, a ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas.

Wata sanarwa da mai ba cibiyar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Ibrahim Abdullahi, ya fitar ta bayyana cewa an tura tawagar ƙwararrun likitoci da jami’an kiwon lafiyar jama’a zuwa ƙauyen Gamji domin gudanar da bincike kai tsaye da kuma daukar matakan kula da wadanda ake zargin sun kamu da cututtuka.

A yayin aikin, tawagar KNCDC ta gudanar da cikakken binciken yaduwar cuta a yankin, inda aka raba su zuwa ƙungiyoyi huɗu, kowacce ƙungiya ta rika ziyartar gidaje daga gida zuwa gida domin gano marasa lafiya, tantance halin da suke ciki da kuma kula da su, domin tabbatar da cewa babu wani gida da aka bari a baya.

Mutanen da aka gano suna nuna alamun rashin lafiya an tantance su ta fuskar likitanci, sannan aka karɓi samfurori daga gare su domin a kai dakin gwaje-gwaje don gano musabbabin cutar da kuma tabbatar da ita.

Baya ga tattara samfurori, tawagar KNCDC ta raba magunguna kyauta ga wadanda abin ya shafa a matsayin matakin gaggawa na kula da marasa lafiya, tare da ba iyalan da ake zargin suna da masu dauke da cuta shawarwarin kiwon lafiya na asali, domin rage haɗari da kuma dakile yaduwar cututtuka masu saurin kamuwa.

Haka kuma, an tara mazauna ƙauyen tare da wayar da kan su kan muhimmancin zuwa cibiyoyin lafiya da zarar sun fara jin alamun rashin lafiya, tare da karfafa musu gwiwar sanar da asibitoci ko jami’an lafiya na yankin da wuri idan sun zargi bullar wata cuta, domin samun daukin gaggawa da kulawa mai dacewa.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce kudirinta na kare lafiyar al’ummar jihar baki ɗaya, tare da tabbatar da cewa KNCDC za ta ci gaba da sa ido kan lamarin, har sai an samu sakamakon gwaje-gwajen dakin bincike, wanda zai jagoranci daukar ƙarin matakai idan bukatar hakan ta taso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here