Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da daukar nauyin aikin hajji da umrah ga magidancin da aka kashe matarsa da ‘ya’yanta shida a yankin Chiranci Dorayi da ke Kano, tare da ba shi sabon gida da cikakken tallafin jin kai domin farfado da rayuwarsa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da wannan mataki ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa iyalin da abin ya shafa, tare da nuna alhini da tabbatar da goyon bayan gwamnatin jihar Kano a gare su.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an kashe wata matar aure da ‘ya’yanta shida a ranar Asabar a unguwar Chiranci Dorayi da ke Kano, inda aka kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin, bayan jami’an ‘yan sanda sun cafke su.
A yayin ziyarar, gwamna Yusuf ya bayar da umarni a bai wa mahaifin iyalin sabon gida mai kyau, tare da daukar nauyin walwalarsa gaba daya, ciki har da taimaka masa ya sake aure idan ya samu abokiyar rayuwa da ta dace, domin ya samu damar sake gina rayuwarsa.
Dangane da shari’a, gwamnan ya umarci babban lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari’a da su gaggauta gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu, inda ya jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci domin a tabbatar da adalci.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa zai sanya hannu kan takardar kisa ga duk wanda aka yanke wa hukuncin kisa a kan wannan lamari na Chiranci Dorayi, tare da tabbatar da cewa irin wannan mataki zai shafi masu laifin kisan Hanifa da kuma wadanda suka aikata kone-konen Gezawa, idan kotu ta same su da laifi.
Ya yaba wa rundunar ‘yan sanda hukumar tsaron farin kaya ta DSS, da sauran hukumomin tsaro bisa hadin kai da gaggawar daukar mataki da ya kai ga kama wadanda ake zargi, sannan ya yi addu’ar Allah ya jikansu da rahama, ya ba iyalansu da al’ummar Kano hakuri da zaman lafiya mai dorewa.













































