Kisan Gilla: Ƴan sanda sun kama magidanci bisa zargin kashe matarsa a Sokoto

Police olopa new 750x430 (1)

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum ɗan shekara 25 mai suna Sufiyanu Aliyu bisa zargin kashe matarsa mai shekara 15, Suwaiba Abubakar, a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Ahmad Rufai, ya fitar a ranar Laraba a Sokoto.

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoba a gidan wanda ake zargin da ke ƙauyen Gwanyal, inda wani mutum ya kai rahoton abin da ya faru ga ‘yan sanda.

Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka killace yankin don gudanar da bincike tare da tattara hujjoji.

An kama wanda ake zargi a wurin tare da wukar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata kisan.

Binciken farko ya nuna cewa rikici ya barke tsakaninsa da matarsa, lamarin da ya kai ga mummunan sakamako har ta rasa ranta.

Jami’in hulɗa da jama’a ya ce an kai gawar matar asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarta, kuma an mika shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin ƙarin bincike.

Rundunar ta tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargi a kotu, tare da jaddada aniyar kwamishinan ‘yan sanda na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da tabbatar da adalci.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here