Kemi Badenoch ta yi Allah-wadai da amincewar Birtaniya da Falasdinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta

Kemi BADENOCH 750x430

Shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya, Kemi Badenoch, ta yi Allah-wadai da matakin ƙasar na amincewa da Falasdinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

A wani faifan bidiyo da Fira Minista Keir Starmer ya wallafa a shafin X a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Birtaniya ta shiga sahun ƙasashe sama da 150 da suka amince da Falasdinu a matsayin ƙasa.

Starmer ya ce ya san irin ɗumamar ra’ayoyi da wannan rikici ke haifarwa.

Sai dai, Badenoch ta mayar da martani da cewa wannan mataki “masifa ne babba,” tana mai jaddada cewa abin tamkar bai wa ta’addanci lada ne ba tare da an ɗora wata sharaɗi kan ƙungiyar Hamas ba.

Ta ce hakan zai bar fursunonin da ke Gaza cikin halin wahala, kuma bai kawo sauƙi ga fararen hula da ke cikin rikicin ba.

Labari mai alaƙa: UNGA: Ƙasashen Birtaniya, Ostireliya da Kanada sun amince da ƙasar Falasdinu

Ta bayyana cewa wannan mataki ya nuna ƙarancin hangen nesa da rashin kyakkyawan shari’a, kuma zai bar dogon nadama ga Birtaniya a nan gaba.

Badenoch ta yi zargin cewa jam’iyyar Labour ba ta iya gyara manyan matsalolin da ƙasar ke fuskanta, ciki har da lafiyar jama’a (NHS), samar da ayyukan yi, da magance matsalar hijira.

A cewarta, saboda gazawar Labour wajen magance waɗannan matsaloli ne suke komawa ga manufofin hagu masu tsattsauran ra’ayi, ciki har da amincewa da Falasdinu a matsayin ƙasa.

Ta kuma yi suka kan tsarin Starmer, tana mai cewa zai bar gwamnatin gaba da babban matsala bayan shekara huɗu na mulki.

A halin yanzu, ƙasashe da dama sun amince da Falasdinu a matsayin ƙasa, musamman ganin yadda ake zargin kisan ƙare-dangi a Gaza.

Amma Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da gwamnatin Amurka sun yi adawa da wannan mataki.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here