Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce ta kama wani likitan bogi mai suna Chidera Ugwu bisa zarginsa da yi wa wata mai juna biyu allura lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.
Mai Magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Karanrta wannan: Zargin almundahana: EFCC ta kama shugabar hukumar NSIP, Halima Shehu
Sanarwar ta ce ta kama likitan bogin na zuwa ne bayan samun wani rahoto kan wani matashi Ukasha Muhammad mai shekara 19 a kauyen Langel da ke karamar hukumar Tofa, wanda ake zargi ya yi wa yar’uwarsa ciki, amma ya hada baki da Chidera domin yi wa matashiyar allura da nufin zub da cikin.
Sai dai a cewar sanarwar, an samu akasi inda allurar da Chidera ya yi wa matashiyar ta yi sanadin mutuwarta.
A cewar rundunar, matasan biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa.
Karanta wannan: Mambobin Hizbullah hudu sun kwanta dama a wani hari ta sama
Wani binciken ‘Yan sandan ya nuna cewa dama ana zargin cewa Chidera ya saba yi wa mata masu ciki allurar da take haddasa mutuwarsu.
Runudnar ta ce za ta gudanar da bincike kan laifin domin tabbatar da adalci.