Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), reshen Kano, ta dakatar da wasu ‘yan majalisar dokokinta guda hudu bisa zargin yi mata zagon ƙasa
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya sanar da dakatarwar da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a Kano.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ‘yan majalisar da aka dakatar suna wakiltar mazabar Kano ta Kudu, Rano/Kibiya, Dala da Rogo/Karaye.
Ya bayyana sunayen ‘yan majalisar da aka dakatar, da suka haɗar da Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Rogo da Kabiru Rurum.
Dungurawa ya ce an bai wa mambobin da aka dakatar da tikitin takara a lokacin zabuka, amma da suka ci zabe sai suka fara abin da bai dace ba.
Ya ba da misali da wani taron da Sumaila ta gudanar a jami’ar sa da ke Sumaila ba tare da gayyato ‘yan jam’iyyar ba a matsayin wani abu na nuna adawa ga jam’iyyar.
Karin karatu: Babu wani dan siyasa mai hankali da zai koma APC-Tambuwal
Ya bayyana cewa za a kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin duk da akwai sauran damar tattaunawa, inda ya ce idan alakarsu da jam’iyyar ta gyaru za a iya sake shigar da su ciki.
NAN ta ruwaito cewa, lamarin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa akwai rikicin cikin gida a jam’iyyar NNPP a jihar Kano inda ake zargin wasu ‘ya’yan jam’iyyar na ganin an mayar da su saniyar ware.