Kano: An kama masu laifi 500, tare da ƙwato makamai, da miyagun kwayoyi 

police officers 750x430

Kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da ayyukan daba da miyagun Laifuka a nan Kano ya kama kimanin mutane 500 da ake zargin ‘yan daba ne da dillalan miyagun kwayoyi a wani mataki na farfado da matasa.

Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne kwamishinan harkokin kimiyya da fasaha, Dakta Yusuf Kofar-Mata, ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a ranar Lahadi a Kano, wanda taron ya mayar da hankali kan karfafa tsarin tsaro a jihar.

Kofar-Mata ya ce kwamitin ya gano gurare masu hadari da maboyar miyagu a cikin al’ummomi da dama a fadin kananan hukumomin takwas, wanda hakan zai bada damar dakile ‘yan daba da safarar miyagun kwayoyi.

Ya kuma jaddada bukatar samar da ingantaccen hadin kai tsakanin kwamitin da shugabannin al’umma domin inganta tsaro, lafiyar ‘yan kasa.

Karanta: Hukumar NDLEA ta kama wani dan kasar Malesiya da ya ɓoye miyagun kwayoyi a cikin manyan na’urorin sauti

A nasa bangaren mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam, ya yabawa kwamatin bisa wannan gagarumin aiki da aka cimma, inda ya bayyana cewa kafa kwamitin ya nuna aniyar gwamnati na magance matsalolin tsaro a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Bakori, ya ce hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro ya samu sakamako mai kyau ta hanyar gudanar da ayyukan sirri.

Don haka ya bayar da shawarar a kafa wata kotu ta musamman da za ta yi shari’ar ‘yan daba, masu satar waya da dillalan kwayoyi.

Har ila yau, kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Abubakar Idris, ya yi kira da a ci gaba da hada kai tsakanin hukumomi domin magance matsalolin tsaro a jihar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here