Kano: Ƴan sanda sun cafke mutane 51 da ake zargi da ayyukan Daba

Police badge (2)

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wasu mutane 51 da ake zargin ‘yan daba ne tare da kwato muggan makamai da miyagun kwayoyi a wani samame da ta kai maɓoyar ‘yan ta’adda a cikin babban birnin jihar.

Ta cikin wata sanarwa a ranar Litinin  da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Hussaini Abdullahi, ya fitar a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori, rundunar ta sanar da faruwar lamarin.

A cewar sanarwar, aikin wanda ya gudana tsakanin ranar Juma’a 13 ga watan Yuni zuwa Lahadi 15 ga watan Yuni ya shafi kananan hukumomin da suka haɗa da: Dala da Gwale da Tarauni inda aka kai samamen a yankunan Kofar Mata da Zage da Kurna da Rijiyar Lemo da Dorayi da Hotoro da kuma Sheka.

Rundunar ‘yan sandan ta ce kai wannan samame na daga cikin sabbin alƙawuran da rundunar ta ɗauka na magance ‘yan fashi da sauran masu laifuka a jihar.

SolaceBase ta ruwaito cewa mutanen da ake zargin, waɗanda aka jera sunayensu da shekarunsu a cikin sanarwar, sun hada da wasu daga sassa daban-daban na birnin Kano wasu daga cikinsu ‘yan shekara 15 ne.

Sanarwar ta kuma yi kakkausan gargaɗi daga kwamishinan ‘yan sandan kan yadda jama’a ke nuna makamai da sunan wasannin gargajiya irinsu Kidan Gangi ko kuma a shafukan sada zumunta da suka haɗa da Tiktok da Facebook da X da har ma da Instagram.

Irin waɗannan ayyukan, a cewar rundunar suna haɓaka ƴan daba da kuma jawo yara ƙanana zuwa aikata laifuka.

Kwamishina Bakori ya yi gargadin cewa iyayen da ke ba wa ‘ya’yansu kariya ko ba su damar ajiye muggan makamai a gida za su fuskanci bincike, tare da masu yin irin wadannan makamai.

Ya bukaci iyaye da masu kula da su da su kasance cikin taka tsantsan tare da kai rahoton duk wani hali da ake da su.

Rundunar ta kuma fitar da lambobin gaggawa don amfanin jama’a wajen kai rahoton aikata laifuka: 08032600299, 08032600300, da 08032600301.

Sanarwar ta karkare da nuna godiya ga hadin kan jama’a wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here