Tsohon dan takarar majalisar tarayya a zaben 2019, Kwamared Adnan Mukhtar Tudun-Wada ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya daina yiwa mahaifinsa talla a Arewa.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Adnan wani jami’in hulda da jama’a kuma malami a jami’a ya bayyana ziyarar buda baki da dan shugaban kasa ke yi a kwanakin nan tare da raba shinkafa a matsayin cin mutunci ga Arewa.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja.
Mukhtar wanda kuma ya nemi zama dan majalisar dokokin jihar Kano a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) yayi kira ga Seyi Tinubu da ya daina rangadin buda baki a Arewa ta hanyar mayar da hankali kan wani abu da zai kyautata rayuwar matasa a yankin a daidai lokacin da ya kamata mulki ya sanya fifiko ba siyasa ba.
Karin karatu: Ɗimuwar rashin samun kujerar minista ce ke damun El-Rufai – APC
“A matsayina na matashi ina so in gaya wa dan Shugaban kasa cewa wannan ba lokacin yakin neman zabe ba ne, shekara biyu kenan a zaben 2027″.
‘’Saboda bai mutunta Arewa, shi ya sa yake raba mana shinkafa kamar mabarata. Wannan ba abin da muke bukata ba ne, Shugaban Kasa ya fito da kudirin gyara Haraji don kawo cikas ga Arewa, hanyar Abuja zuwa Kano ba a kammala ba, masana’antunmu ba su yin aiki, Katsina, Zamfara da wasu sassan Sakkwato ba su da tsaro,” inji sanarwar.
Ya kamata ya sanar da mahaifinsa cewa Arewa na kukan wariya. Ana mayar da mu gefe. A bar shugaban kasa ya magance mana matsalolinmu, amma zuwan nan a ba mu abinci cin mutunci ne.
‘’Ko zai iya yin abubuwa irin haka a Kudu, Legas musamman inda ya fito? ”
‘’Duba yadda yake zaune a fadar sarakunan gargajiyar mu, ba tare da girmamawa ba”.
‘’ Yadda ya yi hannu da hannu da Sarkin Zazzau ba tare da girmama al’adunmu ba. Shin zai iya yi da Oba na Legas ko Oni na Ife haka?
‘’Ina kira ga duk wani matashi mai kishi da ya fito ya nisanta kansa daga ayyukan Seyi Tinubu, wanda ba a zabe shi ba kuma ba ya rike da mukamin siyasa a gwamnatin mahaifinsa.