Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana kafafen sada zumunta a matsayin “kungiyar ta’addanci”.
Sarkin ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a taron kwamitin zartarwa na majalisar sarakunan Arewa karo na bakwai a Maiduguri.
Sarkin ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su bar labaran karya da kage a shafukan sada zumunta ba, domin suna kara tabarbarewar tsaro.
“Dole ne hukumomin tsaro su yi maganin wannan kungiyar ta’addanci da ake kira social media.”
Karin karatu: Hukumar ba da agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin Duniya za ta rufe ayyukanta a Najeriya
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce hare-haren da ake kaiwa Filato da sauran sassan kasar abin damuwa ne kuma yana bukatar kulawa cikin gaggawa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce adadin wadanda suka mutu a harin da aka kai a Filato ya kai 54.
A cewar kungiyar kare hakkin bil adama, daruruwan mutane ne suka rasa matsugunansu tun bayan faruwar lamarin kuma mazauna yankin na cikin fargabar yiwuwar sake kai wani hari.