Kaduna: Gwamna Uba Sani ya karɓi masu ibada a coci su 82 da aka kuɓutar

IMG 20260205 WA0023

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da cewa an kuɓutar da masu ibada 82 da aka sace a lokacin ibadar coci a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A ceto mutane ta hanyar wani tsari na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna, ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa da kuma hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara wajen waɗanda aka kuɓutar a cibiyar kula da mata da yara da ke Kaduna, inda ake basu kulawar lafiya da kuma taimakon farfaɗo da tunani bayan halin da suka shiga.

An sace mutanen ne a ranar da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kurmin Wali yayin da ake gudanar da ibadar coci.

Rahotannin farko sun nuna cewa kusan mutane 177 ne aka sace a lokacin harin.

Gwamna Uba Sani ya nuna alhini ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu, yana mai bayyana harin a matsayin abin firgita, tare da tabbatar wa al’ummar Kurmin Wali cewa ana ci gaba da ƙoƙari domin kuɓutar da sauran mutanen da har yanzu suke hannun masu garkuwa.

Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an kuɓutar da dukkan waɗanda ke tsare tare da haɗa su da iyalansu, yana mai tabbatar da cewa tsaro da lafiyar al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin jihar ke ba muhimmanci.

Gwamnan ya yaba da tsarin tsaron jihar Kaduna, da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa, da hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro, bisa yadda suka gudanar da aikin cikin kwarewa da dogaro da bayanan sirri, tare da ƙarfafa mazauna jihar su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai da sahihan bayanai domin dawo da dawwamammen zaman lafiya a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here