Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wasu kakin sojoji guda 15 da ba a ɗinka ba, tare da tsare wasu mutane biyu da ake zargin barayin mota ne.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Mansir Hassan, ya fitar ranar Talata a
Hassan ya ce, “A ranar 25 ga watan Agusta da misalin karfe 1:20 na rana, a lokacin da jami’an rundunar ke aikin sintiri a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, jami’an ‘yan sanda sun tsayar da wata mota inda suka gano wata baƙar jaka ɗauke da kayan sojoji 15 da ba a dinka ba.
Ya ce, wanda ake zargin ya bayyana cewa zai kai kayan ne ga wani a kauyen Udawa, sannan zai kai su ga ‘yan fashi a yankin Chukuba da ke karkashin karamar hukumar Shiroro ta jihar Nijar domin gudanar da ayyukansu. “A halin yanzu wanda ake zargin yana ba ‘yan sanda hadin kai don kama sauran wadanda ke da hannu a ciki,” in ji shi.
Hassan ya kuma bayyana cewa, a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 12:00 na rana ne ƴan sandan da ke sintiri a yankin, suka ci karo da gungun ‘yan fashi da makami da suka tare hanya ta hanyar amfani da katako da duwatsu. ” Bayan isowar wurin, an yi artabu tsakanin ‘yan sanda da ‘yan fashi da makami. “Karfin wutar da rundunar ‘yan sandan ke da shi ya tilasta wa ‘yan fashin tserewa cikin dajin da ke kewaye. “A yayin musayar, an kashe daya daga cikin ‘yan fashin kuma an kwato bindigarsa da aka yi a gida da kuma harsashi daya,” inji shi. Hassan ya ce ‘yan sandan na ta tseguntawa dazuzzukan dajin a ci gaba da gudanar da aikin cafke sauran wadanda ake zargin. Kakakin ya ce wani Mai suna AbdulAziz AbdulMumin ne ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa an sace motar sa kirar Toyota mai baƙa.
Ya ce, bayan samun rahoton an gano motar a unguwar Hayin Dan Mani da ke karamar hukumar Igabi ta jihar. “Cikin gaggawa ƴan sanda suka bi diddigin lamarin kuma sun ci gaba da sa ido. “Da misalin karfe 8:00 na daren Litinin, ƴan sanda sun shiga tare da kama wasu mutane biyu da ake zargi,” in ji Hassan. Ya ce an damke Abdul Mukhtar da abokinsa, Mamman Ahmad, mazaunin gidan Zoo Road, Kano. “An samu Ahmad yana tukin mota kirar Mercedes Compressor mai lamba AKD 547 GY, wanda kuma ake zargin an sace shi,” inji Hassan. A cewarsa, a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin yin amfani da babbar makullin satar motoci. Ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkar ayyukan wadanda ake zargin da kuma gano sauran masu hannu a ciki. Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Mista Audu Dabigi, ya yaba wa jami’an bisa kyakkyawan aikin da suke yi. Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su da hurumi a cikin jihar.
NAN