Kada ku karaya- Saƙon Tinubu ga ƴan Najeriya

BAT Tinubu 750x430

Shugaba Bola Tinubu, ya amince da cewa har yanzu Najeriya ba ta kai ga inda ake so ba, amma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da sa rai.

Shugaban ya yi wannan roko ne ga ‘yan Najeriya, ta cikin wata sanarwa wadda shi da kansa ya sanya wa hannu a yau Alhamis.

Tinubu ya ce, “lokacin bukuwan babbar Sallah ya na tunatar da mu nauyin da ya rataya a wuyanmu fiye da imani musamman wajen nuna juriya, juriya da tausayi da sadaukarwa ga ci gaban kasarmu abin ƙauna”.

“Duk da cewa tafiyar ba ta yi sauki ba, wasu kuma suka nuna shakkun alkiblar mu, jajircewar shugabannin gwamnati da masu zaman kansu, tare da goyon bayan mafi yawan ‘yan Nijeriya, na samar da sakamako, ina mai tabbatar muku da cewa ranaku mafi tsanani na bayan mu, muna shiga wani sabon zamani na sabon fata da wadata da muka yi alkawari shekaru biyu da suka wuce.

“Watakila har yanzu ba mu kai ga inda muke fata ba, amma ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya da kada su karaya, mu rike imaninmu mu daure gyare-gyaren da muke yi na kara samun karbuwa, tare da manyan alamomin tattalin arziki a yanzu suna tafiya a hanya mai kyau.

Nan ba da jimawa ba, kowa zai ga fa’ida,” in ji sanarwar.

A cewar Tinubu, babban makasudin wadannan sauye-sauye shi ne, ba wai don inganta kididdiga ba ne kawai, a’a, don kawo sauyi ga rayuwa da kuma dora Nijeriya kan turbar ci gaba mai dorewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here