Kungiyar malaman Najeriya NUT, ta buƙaci shugaban kasa Bola Tinubu, da ya ba da fifiko wajen farfaɗo da kimar malamai da walwalar su domin ganin sana’ar su ta zama abin burgewa ga matasa.
Shugaban ƙungiyar ta NUT na kasa, Kwamared Audu Amba, ne ya yi wannan roko a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a Abuja.
Ya buƙaci gwamnati da ta mayar da malamai abin koyi tare da mayar da aikin koyarwa wani ginshiƙin ci gaban al’umma.
Amba ya bayyana takaici kan halin da ake ciki a yanzu inda koyarwa ta zama wani zaɓin ƙarshe a tsakanin masu neman aiki.
Ya ce, ya kamata a sauya sana’ar koyarwa ta yadda za ta zama zabin da matasa ke so.
NAN












































