A wani mataki na ƙarfafa gwiwar matasa musamman ‘yan mata, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bai wa wata yarinya mai suna Joy Ogah damar zama a kujerarsa na ofishin mataimakin shugaban ƙasa na Najeriya na tsawon rana guda.
Wannan mataki na nuna goyon bayan gwamnatinsa ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu wajen inganta ilimin ‘yan mata da tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata.
An gudanar da taron ne a ofishin mataimakin shugaban ƙasa da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja, lokacin da Shettima ya karɓi tawagar ƙungiyar Shirin Ƙasa na Taimakon Yara (PLAN International) ƙarƙashin jagorancin daraktar shirye-shirye da kirkire-kirkire, Helen Idiong.
A lokacin taron, mataimakin shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatin Bola Tinubu tana da cikakken shiri wajen tallafa wa ilimin ‘yan mata a faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa shirin ciyar da ɗalibai a makarantu na daga cikin manyan matakan da ke taimakawa wajen ci gaba da wannan manufa.
Shettima ya bayyana uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a matsayin misali na yadda take kula da ilimin‘yan mata da aka ba damar ilimi da goyon baya kuma za ta iya zama jagora mai nagarta.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati mai ci tana ba da muhimmanci ga haɗin kai da ba wa mata dama a cikin al’amuran ƙasa.
Bayan jawabinsa, Shettima ya bai wa Joy Ogah damar zama a kujerarsa na mataimakin shugaban ƙasa na tsawon rana guda domin ta yi jawabi ga ‘yan ƙasa, inda ta yi kira ga gwamnati, masu tsara manufofi da kungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen inganta ilimin ‘yan mata da kare haƙƙinsu.
Joy ta jaddada buƙatar samar da kayan kula da tsaftar jiki kyauta a makarantun ‘yan mata tare da tabbatar da samun ruwa mai tsafta, tsaftar muhalli da abinci mai gina jiki ga yara a Najeriya.
Ta nuna damuwa cewa a faɗin ƙasar, yara miliyan 10.5 ne basa zuwa makaranta, kuma fiye da kashi 60 cikin ɗari daga cikinsu ‘yan mata ne.
Joy ta bayyana cewa ‘yan mata na iya zama shugabanni idan gwamnati da hukumomi suka aiwatar da manufofi masu ƙarfafa musu gwiwa da ba su damar samun ingantaccen ilimi.
Ta ƙare da cewa duk da cewa ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa na rana guda, ƙoƙarin da take wakilta bai kamata ya tsaya a rana ɗaya ba, domin ya kamata a ci gaba da shi a manufofi, makarantu, tattaunawa da kasafin kuɗin gwamnati.













































